ga wasu hanyoyi 15 Da zakubi wajen inganta tarbiyyar yara
GA WASU HANYOYI (15) DA ZAKU BI WAJEN INGANTA TARBIYYAR YARA
1. KU KOYAR DA YARA GIRMAMAWA
• Yawan gaisheda Na gaba dasu
• Nutsuwa da barin wasa Ahanya
• Fita cikin kyakykyawar shiga
2. KU RABA YA'YANKU DA HALAIYYAR
• Yawan yawace-yawace
• Yawan Abokai / ƙawaye barkatai
• Rashin kunya da faɗace-faɗace
3. KU RINƘA KWAƁAR BAKIN YARANKU
• Idan suna sa baki A maganar manya
• Idan suna kawo tsegumi da gulma
• Idan suna zagi ko ƙaryata manya
4. KUYI MUSU HORO ME TSANANI :
• Idan suna wasa da Sallah
• Idan suka fara kwaɗayi da roƙo
• Idan suka fara ƙarya da lalaci
5. KU ƘARA JAWO YA'YANKU JIKI :
• Idan suka balaga
• Idan basu da lafiya
• Idan kuna gida A zaune
6. KU KWAƊAITAR DA YA'YANKU :
• Nacin karatu da rubutu
• Dagewa wajen cimma buri
• Lada da Nasara in anbi hanyar Allah
7. KU NUNAWA YARA MUHIMMANCIN :
• Riƙo da Addinin Musulunci
• Zumunchi da ziyarar dangi
• Lafiya, Lokachi da kuruciya
8. KU DAINA WAƊANNAN AGABANSU:
• Bayyana tsiraici / Mu'amalar Aure
• Wasan banza na kuruciya, kallo
• Bayyana rashin jituwa Atsakaninku
9. AGABAN YA'YANKU KU YAWAITA :
• Karatan Alƙur'ani da salloli
• Aikata gaskiya da Ruƙon Amana
• Wadatar zuci da godiyar Allah
10. SUKE JIN TSORON KU TA HANYAR:
• Tsawatar musu in sunzo da wargi
• Rashin barinsu babu abinyi
• Taƙaita nuna musu so kuru-kuru
11. KU DAGE KU CIREWA YA'YANKU :
• Tsoron mutuwa
• Tsoron talauci
• Tsoron wanda baya tsoron Allah
12. KU GOYI BAYAN YA'YANKU INHAR :
• Sune ke da gaskiya
• Ba saɓo suka aikata ba
• Sunyi abu domin kare Mutuncinku
13. KU RIKA TSORATAR DA YARANKU :
• Illar Haɗama
• Fitinar rigima
• Haɗarin taƙama da girman kai
14. KU RIKA SANARDA YARANKU:
• Asali da Tarihi
• Mutuwa da ƙabari
• Daɗi da rashin sa
15. KU BAWA YARANKU HORO NA :
• Taƙaita cin abinci
• Taƙaita Bacci da zaman hira.
• Watsarda dogon buri da sharholiya
Allah ya sa idan mun ji mu yi aiki da Abinda mukaji.
Hatimu Abdullahi Ggn
Comments
Post a Comment