JAN HANKALI MAI MATUKAR MUHIMMANCI
Jan Hankali Mai Matukar Muhimmanci
MU KOMA GA ALLAH
1. Da zarar ka tashi za ka bude data don ganin sakon duniya. Amma Sallar Asuba cikin jam'i ta gagare ka.
2. Kana iya minti 90 cikin kallon ball idan an yi rashin sa'a a tafi karin lokaci. Amma Sallar farilla ta gagare ka cikin Jam'i don kallon ball.
3. Kana iya haddace 'handout' don ganin ka ci jarrabawar duniya ta dan Adam, Amma baka iya haddace surah daya ta Alqur'ani don guzurin lahira.
4. Kana da halin kyautar mota don neman suna, Amma baka da hannun kyautatawa gajiyayyu da marayu don neman lahirarka.
5. Kana da lokacin musu, Amma baka da lokacin yi wa Annabi salati.
6. Kana da kudin sayan mota da sutura ta alfarma, Amma sayan tsinsiya ta sharar dakin Allah ta gagare ka.
7. Kana da lokacin karanta jarida, Amma baka da lokacin karanta maganar mahaliccinka.
8. Kana iya kuka don asarar abun duniya, Amma tuna azabar kabari ya gagare ka.
9. Kana da lokacin kallon 'season film', Amma vaka da lokacin sada zumunci tagagarebka, don neman haye siradi.
10. Kana da lokacin zuwa ko ina ne don neman abun duniya, Amma neman ilimin sanin mahaliccinka ya gagare ka.
11. Kai ne jagora wajen zalunci da cin dukiyar al'umma, Amma kiran sallah (Ladanci) abun kunya ne a gareka.
12. Ka zabi rayuwar duniya fiye da ta lahira, bayan ba ka san yaushe za ka mutu ba.
NAZARI NA MUSAMMAN
1. Idan arziki ne ya sanya ka bijirewa mahaliccin ka, to yau ina Karunah?.
2. Idan zallan sabon Allah kake ji da shi da shagaltuwa, to yau ina Fir'aunah?
3. Idan zalunci ka sa a gaba, to yau ina Hamana?
da duniya lafiya.
Comments
Post a Comment