wasu hanyoyin shagwaba miji
Wasu Hanyoyin Shagwaba Miji
Nunawa miji soyayya da kauna, hanya ce ta Shagwaba shi. Shagwaba shi kuwa na kara sa shakuwa da juna. Shi kuma shakuwa nasa soyayya yayi tasiri a tsakanin masoya. Idan kuma soyayya yayi tasiri, rabuwa zai yi matukar wahala ga ma'aurata.
Ga wasu hanyoyi masu sauki da zaki iya Shagwaba mijinki idan kina tare da shi a gida.
1: Ki saba yiwa mijinki tausa a duk lokacin da kika fahimci ya dawo gida a gajiye.
Bayan cin abinci da shiga wanka, samu manki na tausa ki danne masa jikinsq domin ya ji karfi ya wassake.
Idan har zaki jimre yiwa miji hakan, tabbas zaki shagwaba shi.
2: Ki kasance kina masa girki ko hada masa abun sha da kika san yana matukar so.
Ba lallle bane ace a kullum kina cikin wadatar yiwa mijinki irin girkin da kika san yana so ba. Sai dai yana da kyau da kuma amfani kina samun lokaci akai akai kina shirya masa abinci ko abunsha da kika san yana so.
Idan har kika saba yiwa mijinki hakan, yana da matukar wahala ya iya cin abinci a waje. Kai hatta ruwan sha zai yi wuya ya sha idan ba kece kika bashi ba. Hakan kuwa zai sa yaji babu abincin da yake ci yaji dadi sai naki.
3: Kada ki bari mijinki yana fita waje ana masa yankan farce. Haka nan ki tabbatar da cewa kina ware wasu lokaci domin gogewa mijinki kaushin kafarsa.
Mata da dama basu amfani da wannan hanyar a matsayin hanyar jawo soyayyar mazansu ba. Sai dai tabbas duk matar da take da dabi'ar yankewa mijinta farce da kuma goge masa kaushi kafansa. Dole ne tayi tasiri a zuciyar mijinta saboda zata shagwaba shi.
4: Ki fahimci irin fim din da mijinki yake da ra'ayin kallo ki rika samu wani lokaci kuna zama kuyi kallon tare.
Idan mijinki ma'abũcin kallon wasan kwallon kafa ne, ma'ana yana da kulub da yake goyon baya kuma ke baki da ra'ayin ball. Kada ki kushe masa kulub ko kiyi masa mummunan fata na rashin nasara. Yadda wasu mazan suke da son kulub dinsu yana iya sakin ki ma bai sani ba idan zaki shigo masa da zolaye. Don haka idan bazaki goya masa baya ba, kada ki kushe masa abunda yake so.
5: Misali duk ranakun jumma'a ki ware wani lokaci da zaki rika daukan karatu a wajen mijinki idan wanda yafiki illimin addini ne shi.
Domin wannan dabi'ar nasa namiji yaji Kaunar matarsa a zuci ta kuma takaita masa zaman banza na hira a waje a daidai wannan lokacin da suka ware na karatun addini.
Wadannan wasu ne daga cikin abunuwan da mace zata dabi'antu dasu domin ganin ta Shagwaba mijinta da su.
Sirrin Zaman Aure
Comments
Post a Comment