Wasu Kalamai Da Maza Suke Son Jinsu Daga Bakunan Masoyansu

1). Ina alfahari dakai 
Namiji yana son jin cewa yana da kima da matsayi a zuciyar macen da yake so. Idan kika furta wannan, zai ji cewa yana da muhimmanci kuma yana taka rawar gani a rayuwarki.

2). Kayi dacen Iyaye da 'yan uwa 👏
Wannan kalma tana sa namiji jin cewa yana da kyakkyawan asalai. Yana kara masa girmamawa ga iyayensa da iyalinsa, kuma yana jin farin ciki da samun soyayyarki.

3). Nayi dacen samunka a rayuwa: Idan mace ta nuna cewa namiji shi ne mafi dacewa da ita, yana sa shi jin alfahari da kansa. Yana kara dankon soyayya, domin yana ganin cewa ba a yi kuskure da shi ba.

4). Kana sani farin ciki:
Namiji yana son jin cewa yana kawo farin ciki ga masoyiyarsa. Idan kika bayyana hakan, yana karfafa masa gwiwa domin cigaba da kokari wajen faranta miki.

5). Allah Ya maka kyankyawan halitta: 
Komai kyan namiji, yana bukatar jin cewa macensa tana kallonsa da so da sha'awa. Idan kika fada masa haka, yana karawa da kai cika da farin ciki da godiya.

6). Kana karfafamini gwaiwa:
Namiji yana son jin cewa yana taimakawa macensa ta zama mafi kyau. Idan kika nuna cewa yana kara miki kwarin gwiwa, zai dada kokari wajen tallafa miki.

7). Basan yadda rayuwata zata kasance da babu Kai:
Wannan kalma tana nuni da cewa namiji yana da matsayi babba a rayuwarki. Yana sa shi jin cewa ba zai iya maye gurbinsa a zuciyarki ba.

8). Idan ina tare da kai bana shakkar komai ko kowa:
Namiji yana son jin cewa yana ba masoyiyarsa kariya da kwanciyar hankali. Wannan kalma tana kara masa jin nauyin kula da ke da kuma tabbatar da jin dadinki.

9). Bana gajiya da kallonka:
Wannan yana nuni da cewa yana da kyau a idanunki kuma kina jin shauƙi idan kina tare da shi. Yana kara masa kwarin gwiwa da jin soyayyar ki sosai.

10). Kai daban ne cikin maza :
Namiji yana son jin cewa yana da bambanci da sauran maza, kuma yana da wata kima ta musamman a zuciyarki. Idan kika furta haka, zai ji daɗin kansa matuka.

Irin waɗannan kalaman suna ƙara dankon soyayya da kuma kusanci ga masoya. Don haka a kullum ki yi ƙoƙarin furtawa mijinki ko saurayinki kalma guda daga cikin waɗannan domin su ƙara masa farin ciki da jin daɗi.


Comments

Popular posts from this blog

The history of sardauna of Sokoto

scholar's

BALA'IN DA ZAI FARU IDAN AKA HARBA MAKAMIN NUCLEAR!