wasu hanyoyin shagwaba miji
Wasu Hanyoyin Shagwaba Miji Nunawa miji soyayya da kauna, hanya ce ta Shagwaba shi. Shagwaba shi kuwa na kara sa shakuwa da juna. Shi kuma shakuwa nasa soyayya yayi tasiri a tsakanin masoya. Idan kuma soyayya yayi tasiri, rabuwa zai yi matukar wahala ga ma'aurata. Ga wasu hanyoyi masu sauki da zaki iya Shagwaba mijinki idan kina tare da shi a gida. 1: Ki saba yiwa mijinki tausa a duk lokacin da kika fahimci ya dawo gida a gajiye. Bayan cin abinci da shiga wanka, samu manki na tausa ki danne masa jikinsq domin ya ji karfi ya wassake. Idan har zaki jimre yiwa miji hakan, tabbas zaki shagwaba shi. 2: Ki kasance kina masa girki ko hada masa abun sha da kika san yana matukar so. Ba lallle bane ace a kullum kina cikin wadatar yiwa mijinki irin girkin da kika san yana so ba. Sai dai yana da kyau da kuma amfani kina samun lokaci akai akai kina shirya masa abinci ko abunsha da kika san yana so. Idan har kika saba yiwa mijinki hakan, yana da matukar wahala ya iya cin abinci a waje. Kai hatta...